Shehu Muhammed Shehu yana rubuta,

Kwamitin riƙon ƙwarya na ƙungiyar ɗaliban Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, ƙarƙashin jagorancin Comrd Shamsuddeen Muhammad Umar, a ranar Alhamis 27 ga watan Janairu, 2022, sun gabatar wa Jami’i mai kula da lamurran ɗalibai a Jami’ar Ɗanfodiyo, Farfesa Aminu Muhammad Mode; da kyautar taya murna a kan naɗinsa da aka yi a matsayin mataimakin jami’i mai lura da sha’anin makaranta a sabuwar jami’ar ilimi ta Shehu Shagari.
Kyautar dai an gabatar da ita ne ga Farfesa Mode a ofishinsa da ke sashen nazarin harsunan turai da kuma kimiyyar harshe na tsangayar fasaha da ilimin addinin musulunci dake Jami’ar Ɗanfodiyo, Sakkwato.
A cewar shugaban riƙo na ƙungiyar ɗaliban Jami’ar Ɗanfodiyo, Comrade Shamsuddeen, sun yanke shawarar ba shi wannan kyauta ne a madadin sauran ɗalibai domin taya shi murna a kan ƙarin girma da ya samu da kuma karrama shi a kan ƙoƙarin da yake yi a kan ɗalibai.
“Mun yanke shawarar gabatarwa Babanmu da wannan kyauta ne a madadin sauran ɗalibai domin taya shi murna a kan naɗa shi da aka yi a matsayin mataimakin Jami’i mai kula da Sha’anin makaranta a sabuwar Jami’ar ilimi ta Shehu Shagari; da kuma karrama shi a kan ƙoƙarin da yake yi a kan ɗalibai, ” Comrd Shamsuddeen ya bayyana.
Da yake mayar da jawabi dangane da wannan kyauta da aka gabatar masa, jami’in mai kula da harkokin ɗalibai, Farfesa Mode, ya nuna fari cikinsa sosai tare da yin alfahari da wannan kyauta.
Farfesa Mode ya ce, “Ina farawa da godewa Allah (SWA) ! Duk da yake ba abin da nake tsammani ba ne saboda ba su gaya mini ba kuma ba su gaya wa mataimakina na city campus. Ina alfahari da shi sosai sannan muna godiya ga ɗalibai a kan haɗin kai da goyon baya da suke ba mu wajen gudanar da al’amurran ɗalibai na Jami’ar Ɗanfodiyo ”
“Sashen gudanar da lamurran ɗalibai yana jin daɗi da alfahari da goyon bayan ɗalibai da yake samu domin idan ba mu samu goyon bayan ɗalibai ba, yana da wahala mu samu nasara”, inji Farfesa Mode.
Ya kuma ƙara da cewa Jami’ar Ɗanfodiyo Jami’a a ce babba domin ta yaye ɗalibai waɗanda suka zama gwamnoni, ƴan majalissa, sanatoci, ƴan kasuwa da dai sauran muƙamai makamantan waɗannan. ya kuma ce za su ci gaba da aiki tare domin samun ci gaban wannan Jami’a ta Ɗanfodiyo .
Daga ƙarshe, ya yi kira ga ɗalibai da su ci gaba da zama lafiya da kuma biyayya ga dokokin makaranta, sannan su ci gaba da karatu domin cimma manufofin da aka sa a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *