Shehu Muhammed Shehu yana rubuta,
Kwamitin riƙon ƙwarya na ƙungiyar ɗaliban Jami’ar  Usmanu  Ɗanfodiyo, Sakkwato,  ƙarƙashin jagorancin Comrd  Shamsuddeen  Muhammad Umar,  a ranar Alhamis 27 ga watan Janairu,  2022, sun gabatar wa Jami’i mai kula da lamurran ɗalibai a Jami’ar Ɗanfodiyo,  Farfesa Aminu Muhammad Mode; da kyautar taya murna a kan naɗinsa da aka yi a matsayin mataimakin jami’i mai lura da sha’anin makaranta a sabuwar jami’ar ilimi ta Shehu Shagari. 
Kyautar  dai an gabatar da ita ne  ga Farfesa Mode a ofishinsa da ke sashen nazarin harsunan turai da kuma kimiyyar harshe na  tsangayar fasaha da ilimin  addinin musulunci dake Jami’ar Ɗanfodiyo, Sakkwato. 
A cewar shugaban riƙo na ƙungiyar ɗaliban Jami’ar Ɗanfodiyo,  Comrade Shamsuddeen, sun yanke shawarar ba shi wannan kyauta ne a madadin sauran ɗalibai domin taya shi  murna  a  kan ƙarin girma da ya samu  da kuma karrama shi a kan  ƙoƙarin da yake yi a kan ɗalibai. 
“Mun yanke shawarar  gabatarwa Babanmu da wannan kyauta  ne a madadin  sauran ɗalibai domin taya shi murna a kan naɗa shi da aka yi a matsayin mataimakin Jami’i mai kula da Sha’anin makaranta a sabuwar Jami’ar ilimi ta Shehu Shagari; da kuma karrama shi a kan ƙoƙarin da yake yi a kan ɗalibai, ” Comrd Shamsuddeen ya bayyana. 
Da yake mayar da jawabi dangane da wannan kyauta da aka gabatar masa,  jami’in mai kula da harkokin ɗalibai,  Farfesa Mode,  ya nuna fari cikinsa sosai tare da yin alfahari da wannan kyauta. 
Farfesa Mode ya ce, “Ina farawa da godewa Allah  (SWA) !  Duk da yake ba abin da nake tsammani ba ne saboda ba su gaya mini ba kuma ba su gaya wa mataimakina na city campus.  Ina alfahari da shi sosai sannan muna godiya ga ɗalibai a kan haɗin kai da goyon baya da suke ba mu wajen gudanar da al’amurran ɗalibai na Jami’ar Ɗanfodiyo ” 
“Sashen gudanar da lamurran  ɗalibai yana jin daɗi  da alfahari da goyon bayan ɗalibai da yake samu domin idan ba mu samu goyon bayan ɗalibai ba,  yana da wahala mu samu nasara”,  inji Farfesa Mode. 
Ya kuma ƙara da cewa Jami’ar Ɗanfodiyo Jami’a a ce babba domin  ta yaye ɗalibai waɗanda suka zama gwamnoni,  ƴan majalissa,  sanatoci, ƴan kasuwa da dai sauran muƙamai makamantan waɗannan.  ya kuma ce za su  ci gaba da aiki tare domin samun ci gaban wannan Jami’a ta Ɗanfodiyo . 
Daga ƙarshe,  ya yi kira ga ɗalibai da su ci gaba da zama lafiya da kuma  biyayya ga dokokin makaranta,  sannan su ci gaba da  karatu domin cimma manufofin da aka sa a gaba.

