Daga Shehu Muhammed Shehu

 

A ranar Litanin, 16 ga watan Oktoba, 2023, cibiyar ƙirƙira da bunƙasa aikin jarida ta Center For Journalism Innovation and Development CJID ta soma bayar da horo na kwana huɗu ga ƴan jaridar makaranta  da ɗalibai masu nazarin aikin jarida a jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo dake Sakkwato, a ɗakin taro na tsangayar kimiyyar zamantakewar ɗan Adam dake jami’ar.

A lokacin da PEN PRESS ke zantawa da babbar jami’ar shirin bayar da horon ta cibiyar CJID kuma Editar jaridar Campus Reporter, Iretomiwa Dele-Yusuf, ta ce bayar da horon wani ɓangare ne na shirin bayar da horo na cibiyar inda suke horas da ƴan jaridar makaranta da kuma ɗalibai masu karatun aikin jarida a kusan dukanin manyan jami’oin Nijeriya da sauran ƙasashen yammacin Afirika.

Iretomiwa Dele-Yusuf daga CJID

Iretomiwa ta ce “kawo yanzu mun horas da ɗalibai da dama a kan aikin jarida a jami’o’i da yawa a Nijeriya da suka haɗar da: jami’ar jihar Legas da jami’ar lbadan da jami’ar tarayya dake Lokoja da dai sauransu domin ƙara tabbatar da gaskiya da adalci.”

Ta ci gaba da cewa sun fito da wannan shiri ne domin sun fahimce cewa a makarantu da dama ana koyar da kwas ɗin aikin jarida amma ɗalibai ba su samun damar a koyar da su a aikace, wannan ya sa suka ɓullo da wannan tsari domin koyar da ƴan jaridar makaranta da ɗalibai masu nazarin aikin jarida a aikace a kan duk wani nau’i na aikin jarida a zamanance.

Ta bayyana cewa bayan kammala horon,  za a tallafa wa ɗaliban da wasu ƴan kuɗaɗe domin su riƙa samar da labarai a makaranta kuma za su riƙa wallafa labaran a shafinsu na Campus Reporter.

Ta ce “bayan sun gama karɓa horo za mu tallafa masu ta hanyar ba su ƴan kuɗaɗe domin samar da labarai da za mu riƙa wallafawa a Campus Reporter, za mu kuma haɗa su da ƙwararrun ƴan jarida domin samun ƙwarewa a fannin ta yanda kafin su kamma karatu sun goge sosai ba sai sun tsaya jiran aikin gwamnati ba”.

Bugu da ƙari ta ce ita ma ta soma aikin jarida ne tun lokacin da take karatu a jami’a inda ta rubutu  labarai masu dimbin yawa,  ta kuma buƙace ɗaliban da su mayar da hankali a kan horon.

Shi ma da yake magantawa, shugaban ƙungiyar ƴan jaridar makaranta ta ƙasa reshen jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo dake Sakkwato,  NACJ, Abdulwasi’u Olokooba,  ya bayyana farin cikinsa a kan shirin, inda ya ce wannan abu ne da suka daɗe suna jira tsawon lokaci.

“Mun yi farin cikin sosai da samun wannan shiri saboda abu ne da muka daɗe muna jiran mu samu a wannan makaranta sama da shekara huɗu”, in ji shi, yana mai cewa tabbas wannan abun maraba ne kuma abin alfarin a gare sa.

Toafeeq Imam, ɗalibin kimiyyar siyasa ne dake matakin aji ukku kuma yana ɗaya daga cikin mahalarta horon,  ya ce ba shakka wannan babban abun ci gaban ne a gare sa.

“Tabbas wannan abun ci gaba ne a gare ni a matsayina na ɗaya daga cikin mahalarta taron, wannan wata dama ce a gare ni ta ƙara samun kwarewa sosai a kan aikin jarida da nake da sha’awa a kansa” Taofeeq ya bayyana cike da farin ciki.

Yanzu haka dai ɗalibai 52 ne maza da mata ke ci karɓa horon na kwana 4 da aka soma ranar Litanin 16 ga watan Oktoban 2023 kuma zai kammala ne a ranar Alhamis 19 ga watan Oktoban 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *