Shehu Muhammed Shehu ya rubuta,
Ɗaliban Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato, a ranar Lahadi 2 ga watan janairu, 2022, sun gudanar da bukin nuna al’adu a makarantar inda aka gayyato ƙungiyoyin ƙabilu daban-daban da ke makarantar domin nuna al’adunsu.
Bukin na nuna al’adu wanda kwamitin riƙon ƙwarya na ƙungiyar ɗalibai suka shirya kuma aka gudanar da shi a ɗakin karatu na MH2, ya haɗa ƙungiyoyin ƙabilu har guda shida waɗanda suka gabatar da al’adunsu daban-daban a gaban ƴan kallo.
Daga cikin wakilan ƙungiyoyin ƙabilu da suka shiga bukin akwai : ƙungiyar ƙabilar Hausawa da Oduduwa da Oyo da lbra da Nupe da kuma ƙabilar Fulani. Duka waɗannan ƙungiyoyi sun gabatar da al’adunsu ne a gaban jama’a cikin tsanaki da kuma wasa da raha.

Cikin ƙungiyoyin ƙabilu shida da suka shiga cikin wannan buki na nuna al’adu, ƙungiyar ƙabilar Fulani ce ta zo ta ɗaya da maki 87.75, inda kuma aka ayyana ta a matsayin wadda ta fi kowace ƙayatarwa wajen nuna al’adunta. Sai kuma ƙungiyar ƴan ƙabilar Nupe waɗanda suka zo na biyu sun samu maki 80 wajen ƙayatar da ƴan kallo da al’adunsu , yayin da ƙabilar Oduduwa ta zo ta ukku da maki 54.75.

A lokacin da Pen Press ta tuntuɓe magatakarda na ƙungiyar Fulani, Comrd. Aliyu Usman Shehu (Minista) dangane da nasarar da suka samu, ya ce sun yi farin ciki sosai kuma suna godiya ga Allah da ya ba su wannan nasara. “Alhamdulillah! gaskiya mun ji daɗi ganin cewa wannan shi ne karo na farko da muka ga wannan da idonmu kuma mun yi nasarar haɗa kan ‘yan uwanmu cikin kwana biyu har muka samu wannan nasara”, Minista ya bayyana.
Ya kuma ƙara da cewa, ” daga cikin al’adun da muka nuna har muka samu nasara akwai: al’adar damun fura, sannan da sarkinmu Arɗo da sutura da rawa da kuma al’adar shaɗi ko sharo”. Daga ƙarshe ya yi kira ga ƴan uwansa Fulani da su ba da haɗin kai da goyon baya wajen ciyar da wannan ƙungiya gaba sannan su mayar da hankali a kan karatunsu.

Haris Abdullahi, shi ne jami’in walwalar jama’a na kwamitin riƙon kwarya na ƙungiyar ɗaliban Jami’ar Ɗanfodiyo,ya ce sun shirya wannan buki ne domin ƙara haɗa kan ɗalibai da kuma nuna muhimmancin al’adu a cikin al’umma.

“Mun shirya wannan buki ne domin mu nuna wa mutane al’ada ita ce ginshiƙin zaman lafiya duba da irin yanayin da muka samu kanmu a Najeriya na rigingimun ƙabilu , shi ya sa muka gayyoto dukan ƙabilun da ke cikin makaranta su zo su nuna al’adunsu domin ƙara haɗa kan ɗalibanmu, ” A cewar Comrd Haris Abdullahi.
Daga ƙarshe, an bayar da kyautuka ga ƙungiyoyi ukku da suka yi wa tsara-zarra inda ƙungiyar ƙabilar Fulani ta kasance Zakaran Shekarar 2021 wajen bukin nuna al’adu na ɗaliban Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *