Shehu Muhammad Shehu ya rubuta,
Aisha Musa Dalil, wadda take ajin farko a sashen koyon harsunan Ingilishi da Faransanci a Jami’ar Umaru Musa Ƴar-Aduwa, Katsina, ta yi nasarar lashe gasar “Hikayata”. Hikayata dai rubutu ne na gajerun labaru na mata zalla wanda sashen Hausa na Bbc ke shiryawa a kowace shekara domin haɓakawa da kuma inaganta adabin Hausa tare da baiwa mata dama su gwada basirarsu ta wannan haujin.
A ranar Jumu’a 26 Nuwamba, 2021, aka ayyana Aisha Musa Dalil, a matsayin wadda ta samu nasarar lashe gasar, bayan da Bbc Hausa ta ayyana labarinta mai taken “Haƙƙina” a matsayin wanda ya fi kowane yin fice daga cikin sauran labarai.
“Haƙƙina” labari ne da aka gina kan wata matashiya mai suna Fatima, wadda mijin mahaifiyarta ya yi mata dukan iska tare da yi mata fyade wanada ya yi sanadiyar ta samu raunuka. Maimakon mahiafyar ta nemo mata magani tare da kai ƙarar mijin a kotu; sai ta rufe ta a ɗaki ta kuma gargaɗe ta a kan kar ta sanar da kowa abin da ya faru da ita. Kamar yadda aka ruwaito a shafin bbc Hausa.

A cewar mahaifiyar Fatima, na ƙi bayyana abinda ya faru ne saboda “rufin asirinki da ni, idan na faɗa, ni da ke tamkar mun kashe kanunmu ne, wa zai aure ki wa zai aure ni”? In ji mahaifiyar Fatima.
Marubuciyar ta yi ƙoƙarin fito da irin matsalolin fyaɗe da yankin Arewa ke fama da su inda masu fama da irin wannan matsala ke tsoron bayyana abinda ya faru da su domin gudun tsangwama daga sauran jama’a.
Aisha Musa Dalil, bafulatana ƴar shekara 18 kuma ƴar asalin Adamaw, sai dai an haife ta kuma ta girma ne a garin Kaduna. Ta ce, ta fara rubutu a shekarar 2018, kuma tana matuƙar sha’awar karanta labarun sarauta.
A kalamanta, ” Tun ina yarinya ina da baiwar ƙirƙirar labaru in rubuta ko in bai wa mutane. Hakan ya sa ni ginu a kan son rubuta labarai.
“Ƙalubalen da ƴan uwana mata ke fuskanta a wannan ƙarni da muke ciki yana daga cikin manyan dalilan da na ƙarfafa rubutuna,” In ji Aisha .
Aisha ta yi waɗannan kalaman ne a bukin bayar da kyautuka ga gwarazan gasar na wannan shekara wanda ya gudana ranar Jumu’a 26 ga watan Nuwamba, 2021, a Abuja, Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *